Countdown
Connect with us

Labarai

HAJJ 2022: Jihar Kaduna ta sake yin rashi daya daga cikin alhazan ta a kasar Saudiya

Published

on

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, ta sanar da rasuwar daya daga cikin alhazan ta, mai suna Hajiya Maryam Ahmad, daga Karamar Hukumar Igabi.

Da yake sanar da rasuwar ta, shugaban hukumar ya bayana cewa Allah ya karbin ran Hajiya Maryam Ahmad a asibiti a garin Makkah.

Shugaban ya Kara da cewa mamaciyar ta na fama da wasu damuwa tunkafin zuwan ta aikin hajji, wanda suka hada da hawan jini da kuma tari wanda take kai da har tayi tarin jini.

Hukumar ta gazarya da Hajiya Maryam asibiti a garin Makkah, domin duba lafiyar ta inda daga bisani rai yayi halinsa.

Rasuwar na ta, ya ba da adadin rasuwar mutum biyu kenan na mahajata jihar Kaduna a hajjin bana.

Akwai Hajiya Asiya Aminu, daga Karamar Hukumar Zaria, wace ita ma ta rasu a aikin hajjin bana.

Zafafa Labarai