Countdown
Connect with us

Labarai

Gwamnatin taraya ta Sanya ranar da jirgin Kasa Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki

Published

on

Gwamnatin taraya ta Sanya ranar litini 23 ga watan Mayu, 2022 a matsayin ranar da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna zai dawo bakin aiki.

An dai dakatar da aikin jirgin kasa ne tun a watan Maris, 2022 biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka Kai ma jirgin a hanyar sa ta zuwa Kaduna, wanda harin yayi sanadiyar mutuwar fasijoji tare da jikata wasu da kuma gar kuwa da wasu fasinjoji.

A wani sanarwa dauke da sa hanu Mai magana da yawun bakin Hukumar Kula Da Sufufurin Jirgin Kasa (NRC), Yakubu Mahmud, yace ” sanar da dawowar aikin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna, ba yana nufi ba za a cigaba da yunkuri ceto fasinjoji dake tsare a hanun ‘yan bindiga da suka sace su ba.

Sanarwa ta jaddada cewa, Gwamnatin na tabatar ma da yan uwan fasinjoji dake tsare a hanun ‘yan bindiga cewa, ceto Yan uwan su cikin koshin lafiya na da matukar mahimanci kuma shine abin dake gaba a gun gwamnatin, tare da cewa kada su dauka dawowar aikin jirgin kasa a matsayin sharewa ko mantar wa ko aje batun kokarin ceto yan uwa nasu.

Sanarwa ta qara da cewa” an dauki tsauraran matakai na gun tabatar da tsaron jirgin ba ma na Abuja zuwa Kaduna kadai ba, dukan jiragen kasa da ke aikin sufuri na jigilar mutane.

Hukumar ta roki hadin kan mutane tare da ba su hakuri su bi dukan sabin shirye shirye da aka fito da su wanda zai taimaka wa hukumar gurin ganin ta inganta aikin sufuri jirgin kasa.

Ta kuma bukace jama’a dasu tabatar da sunbada numbobin bayanan katin zama dan kasa (NIN), a yayin siyan tikitin hawa jirgin kota yanar gizo ko a tashohin jirgin, tare da samar da numbobin wayar ma kusantan su.

Zafafa Labarai