Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Gwamnatin Kaduna Ta Nada Sabin Shugabanin Wasu Hukumomi guda hudu

Published

on

Gwamna Jihar kaduna, Mal. Nasiru Elrufai, ya amince da nada wa su sabin shugabanin wasu hukumomi guda hudu a Jihar, domin Cike gurbin da ke a kwai.

Sabin Shugabanin hukumomi sun hada da hukumar kula da aikin alhazai na Jihar, shugaban hukumar kididiga, Mai bada shawara a bangaren siyasa da kuma shugaban kula da harkar ingancin illimi a fadin makarantu Jihar.

Bayanin haka ya fito be daga wata sanarwa dauke da sa hanun mai bawa gwamna shawara akan kafafen sadarwa, Muyiwa Adekewe, inda sanarwa ke bayana cewa “
Baba Bukar Alhaji, shine shugaban hukumar kididiga (Statistician General), Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, shugaban hukumar Alhazai, Abdullahi Muhammad Ibrahim, Mai bada shawara Kan harkokin siyasa sai kuma Adama Abdullahi Wada, a matsayin jagoran kula da inganci karatu makarantu dake fadin Jihar.”

Nadin nazuwa me a daidai lokacin da wa’adin mulkin gwamnatin ke matakin na dab da zuwa karshe wa’adi da kundin tsarin mulki kasa ya tanada.

Zafafa Labarai