Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Gwamnatin Kaduna ta bai wa yan kasuwa Sabo Tasha wa’adin mako daya su tashi domin sabonta kasuwar

Published

on

Ismail Umar Dikko
DG KASUPDA

Hukumar tsare-tsare da raya birane kaduna (KASUPDA), ta Bai wa yan kasuwar sabon Tasha dake karamar hukumar chikun, wa’adin mako guda da su tatara kayan su domin ba gwamnati dama sabonta gine gine kasuwar.

Bayanin hakan na kushe ne a wata takarda sanarwa da hukumar ta fitar a ranar 12 ga watan mayu, 2022 dauke da sa hanun Darekta Genar na hukumar, Ismail Umar Dikko.

Sanarwa ta bayana cewa” a karkashin shirin sabonta birnin Jihar kaduna wanda ya hada da sabon gine-gine ko sabon ta tsofin gurare, Wanda ya hada da kasuwar sabon Tasha.

A don haka, ake bukatar al’umar kasuwan da su kwashe inasu-inasu, su tashi da ga kasuwar a cikin mako guda.

Rashin yin hakan zai ba hukumar damar tashin kasuwar da kanta Kamar yadda doka sashe na 62 saki layi na 2 da Kuma sashe na 62 na dokar kaduna master plan, na shekarar 2016 ya tanadar.

Zafafa Labarai