Countdown
Connect with us

Illimi

Gwamnatin Kaduna Na Daf Da Kamala Gina Makarantun Sakandare Kwana Na Kimiya Guda Shida

Published

on

Halima lawal

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce aikin gina makarantun kwana na kimiyya guda shida wanda yasa mu tallafin kudi daga bankin ci gaban Musulunci (IsDB) ya kai kashi 98 cikin dari Kamar yadda jaridar inside kaduna ta walafa.

Kwamishiniyar ilimi, Madam Halima Lawal, ce ta bayyana haka a Kaduna a wajen bude horon kwanaki biyar ga malamai da jami’an sa ido da tantancewa da masu kula da makarantu.

Kwamishinan wanda ta samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, Dakta Haliru Soba, ya bayyana cewa makarantun guda biyu ne a kowace gundumomin Sanata, daya na maza daya na mata, a dukan nin gundumomin sanatoci uku.

A cewarta, manufar ita ce inganta ilimin kimiyya da kuma kara yawan wadanda zasu Yi karatun a fanin da nufin bunkasa ilimin da ake bukata a fannin kimiyya domin ci gaban jihar.

Ta ce, makarantun sun hada da gudamar: Hunkuyi a karamar hukumar Kudan; Pambegua a karamar hukumar Kubau; Rigachikun a karamar hukumar Igabi, Buruku a karamar hukumar Chikun, Jere a karamar hukumar Kagarko da Manchok a karamar hukumar Kaura.

“Makarantun suna da dabarun samar da kayan aiki na zamani daidai da ka’idojin duniya don ba da ingantaccen ilimin kimiyya,” in ji ta.

Kwamishinan ta ce horon na daga cikin bangaren inganta aikin ga malamai da masu kula da makarantu da kuma jami’an sa ido da tantancewa.

Ta ce horon zai kunshi ingantattun hanyoyin koyarwa, tsare-tsare, dubawa, sa ido da tantancewa.

Ta yi nuni da cewa, horon zai shirya wa mahalarta taron don biyan bukatun tsarin bayar da ilimin makarantun sakandare a halin yanzu.

Tun da farko, manajan aikin, Mista Shehu Isah, ya ce malamai 321, masu kula da makarantu da kuma sifetoci ne ke halartar horon.

Isah ya ce, daga cikin mahalarta taron guda 321, 270 malamai ne, wadanda suka kunshi malaman kimiyya 90 da malaman da ba na kimiyya ba 180.

Ya ce daga cikin malamai 270, an zabo 180 daga sabbin makarantun sakandire da aka gina yayin da sauran 90 kuma an zabo su ne daga makarantun sakandaren da ake da su a fadin jihar.

Zafafa Labarai