Countdown
Connect with us

Illimi

Gwamnati Kaduna to kori shugaban NUT tare da malaman firamare sama da 2,000

Published

on

Hukumar kula da illimi bai daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB), tace ta salami malaman firamare 2,357 sakamokon fadi jarabawa chanchanta da tayi musu.

Mai magana da yawun hukumar, Hauwa Muhammad, ta sanar da haka ranar lahadi, a kaduna, tace sun gudanar da Jarabawar ga Malamai firamari akala 30,000 a watan disamba 2021.

Malamai firamari 2,192 tare da shugaban NUT Mista Audu Amba, an Kore su aikine bisa kin zuwa zana jarabawa, injita.

Muhammad, tace Malamai 165 suku ma a salame su ne bisa rashin nuna kwazo a jarabawa chanchanta.

In za a tuna a shekara 2018, Gwamnatin Kaduna ta Kore Malamai 21,780 sakamakon fadi jarabawa chanchanta, inda ta maye gurbin su da sabin Malamai 25,000.

Har ila yau, a watan disamba 2021, hukumar ta kori Malamai 233 bisa zargin takardun boge.

Zafafa Labarai