Countdown
Connect with us

Labarai

Gwamnati Kaduna tayi wasu sabin nade nade don tayata aiki

Published

on

Gwamna Jihar Kaduna, Nasiru Elrufai

Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagoranci Gwamnan Nasir El-Rufai, tayi wasu Sabin nade nade, domin tayata gudanar da aikin ta.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Alhamis ya ce Umma za ta maye gurbin Dr. Shehu Muhammad, wanda ya ajiye aiki domin yin takarar kujerar siyasa.

Sai tsohon kakakin majalisar jihar, Aminu Shagali a matsayin mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa.

Bayan haka, Hajiya Umma Ahmed, kantomar karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kwamishinan harkokin kananan hukumomin jihar.

Shi kuma Abdullahi Ibrahim wanda shine mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa zai canja Umma a Birnin Gwari.

Murtala Dabo kuma shine sabon mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tattalin arzikin jihar.

El-Rufai ya nada Dr Jibrin Alhaji babban sakataren hukumar majalisar dokokin jihar.

Zafafa Labarai