Countdown
Connect with us

Labarai

Gwamnati Kaduna tafasa karban kudin haya domin gudanar da sallar idi a dandalin Murtala

Published

on

A jiya Alhamis, ne labari ya karade shafukan sada zumunta, inda aka ga hukumar kula da kasuwani ta Jihar Kaduna ta fitar da sanarwa biyan kudin haya dayakai kimani #500,000 kafin gudanar da sallah idi a dandalin Murtala dake birnin Kaduna.

Lamarin yazo da abubuwan ban mamaki domin shine karon farko da yafku a Jihar Kaduna.

A rahotonin da Kadunareporters ta taro, Jama’a da dama daga ciki da wajen Jihar Kaduna ne suka dinga tofa albarkacin bakin su tare da cike da mamaki.

Masalacin doka dake cikin birnin Jihar kaduna, suke gudanar da sallar idi a dandalin Murtala a duk shekara Kama daga karamar ko baban sallah.

a yayin fira da daya daga cikin ‘yan kwamiti masalaci da jaridar BBC HAUSA tayi, ya tabatar da cewa lamarin yazo musu da abun mamaki domin sun dade suna gudanar da sallar idi su a dandalin Murtala ba kuma a taba cewa subiya ko sisi ba.

Daga bisani dai Gwamnati Jihar Kaduna ta fito ta janye maganar karban kudi a wani sabon sanarwa da hukumar kulada kasuwani ta fitar.

Saidai rahotonin suna nuni dacewa Dan takarar kujera majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Hon. Samaila Sulaiman ya tura ma kwamiti masalaci kudin biyan haraji.

Kamar yada hoton biyan kudin take ta karakaini a kafafen sada zumunta, saidai Kawo yanzu ba mu samu tabacin sahihanci biyan kudin daga bangaren Hon. Suleiman ko masalaci da aka bawa kudin ba.

Zafafa Labarai