Countdown
Connect with us

Rahotoni

Gwamnati Kaduna ta umarci dakatatun Ciyamomi Giwa da Chikun su dawo bakin aiki, domin dakatawar su ya saba ma kudin tsarin mulki

Published

on

Ciyamomi Giwa da Chikun Hoto: Kaduna political Affairs Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da zababbun shugabannin kananan hukumomin Chikun da Giwa, Mista Salasi Musa da takwaransa Abubakar Lawal cewa su ci gaba da gudanar da ayyukansu, tare da bayyana cewa dakatarwar da majalisar ta yi musu ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma tsarin mulki dokokin jihar Kaduna.

Idan dai za a iya tunawa majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi bisa zargin karkatar da kudade.

A fusace da faruwar lamarin, shugabannin da aka dakatar sun tuntubi gwamnatin jihar kan lamarin.

Sun rubuta wa Babban Lauyan Jihar, inda suka bukaci a yi musu tafsiri da shawarar shari’a kan dakatarwar da aka yi musu.

A nata martanin, babban mai shigar da kara kuma kwamishiniyar shari’a, Aisha Dikko, ta bayyana cewa dakatar da shugabannin kananan hukumomin biyu “karara ce ta sabawa duk wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara) da kuma dokar kananan hukumomin jihar Kaduna.”

Ta bayyana cewa dokar ta tanadi cewa ‘’Majalisun kananan hukumomi kungiya ce mai zaman kanta ta gwamnati sannan kuma suna da zababbun ‘yan majalisarsu.

A cewarta, an tsara hanyoyin da za a bi wajen tsige shugaba da mataimakin shugaban karamar hukumar a jihar bisa dokar kananan hukumomin jihar Kaduna ta 2018.’’

Dangane da shawarar da ke kunshe a cikin wata wasika mai kwanan watan Yuni 14, 2022, mai lamba SSG/KDS/276/VOL 1, Sakataren Gwamnatin Jihar ya rubuta wa shugabannin biyu, inda ya umarce su da su koma ofisoshinsu.

Zafafa Labarai