Countdown
Connect with us

Labarai

Gwamnati Kaduna ta rufe otal dake baiwa dilalan mugan kwayoyi masauki

Published

on

Gwamna Nasiru Elrufai Hoto: Insidekaduna Asali: Insidekaduna

Gwamnati Kaduna ta rufe wani otel me suna ” Holiday Conference Hotel” dake cikin birnin Kaduna bisa zargin baiwa dilalen mugan kwayoyi masauki, tare da kin biyan kudin harajin fili na tsawon shekaru biyar.

Jaridar Voiceofliberty ta rawaito cewa, Kwamishina Kasuwanci, kirkira da Fasaha, Prof. Kabir Mato, ne ya sanar da haka yayin zantawa da manema labarai a kaduna.

Mato yace andai rufe otal din ne a ranar 15 ga watan yuni 2022, domin ya zama cibiyar bata zamantakewa.

Yakara dace mutane na ziyarta otal din domin siye da shan mugan kwayoyi, Kuma yarjejeniyar izini Kasuwanci da ke tsakanin otal din da Gwamnati Jihar Kaduna na shekara 15, wanda ya kare a watan Faburairu 2022.

Tun daga shekara 2017 otal din ya daina biyan kudin harajin yarjejeniyar sa ga Gwamnati Kaduna, cewar Kwamishina.

Mato, yayi jinjina ma Yan kasuwan da sukayi rijista muhalin Kasuwanci su da Gwamnati, domin hakan na taimaka wa ministirin sa gudanar da ayyuka ta yada yakamata.

Ya kuma shawarci duk Yan kasuwa da basuyi rijista ba da suyi kokarin yin domin bin ka idar dokakin Jihar, rashin yi ka iya haifar da rashin samun damamakin Kasuwanci.

Zafafa Labarai