Countdown
Connect with us

National

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan ikirarin Gwmana Ortom

Published

on

Fadar shugaban kasa tayi martani kan ikirarin da Gwmana jihar benuwai Samuel Ortom yayi na cewa shugaban kasa yahana jami’an tsaro kada su dau mataki kan makiyaya da suka adabi jiharsa.

Gwamna wanda ya bayana hakan a kafafen watsa labarai yace wani baban jami’in soja ne ya fada masa cewa shugaban kasa ya bada umarni kada su dau mataki kan makiyaya da ake zargin kan tashin hanukala baya bayan nan.

Sai dai a cewar fadar shugaban kasa, sam bataji dadin furicin gwmana ba.

Maganar Gwamna maganace da bata da tushe a cewar Garba Shehu, kakakin shugaban kasa.

“Idan yana son ya nuna cewa shi jarumi ne kamar yadda ya yi ikirari to ya bayyana sunan jami’in sojan da ya ba shi wannan labari ko ya yi shiru da bakinsa,” a cewarsa.

Zafafa Labarai