Countdown
Connect with us

Labarai

Elrufai ya kadamar da shirin raba gidan sauro na shekarar 2022

Published

on

Elrufai yayi kadamar da shirin raba gidan sauro. Hoto:The Governor Of Kaduna State Asali: Facebook

Gwamna Jihar Kaduna, Mallam Nasiru Elrufai, a ranar laraba 6 ga watan yuli, 2022 ya jagoranci kadamar da shirin raba gidajen sauro ga al’umar Jihar.

Ana sa ran shirin zai raba gidajen sauro da yakai sama da miliyan biyar ga yan Jihar, don yakar ciwon maleria.

Shirin wanda zai gudana daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Yuli, 2022.

A yayin jawabin sa, Elrufai ya bayana mahimanci amfani da nets din sauro gun yakar ciwon maleria.

” Yakar zazabi ciwon sauro aiki ne ga remu baki daya, nets din na dauke da sinadarin dake kashe saura da yazo kusa da net din tare da ba da kariya ga cizon sauran, a don haka zamu cigaba da wayar Kai al’umar Jihar a lungu da sako mahimanci amfani da gidan sauro.”

Ana ta jawabin, Kwamishina Lafiya ta Jihar, Dr. Amina Baloni, ta bayana cewa Jihar Kaduna ta samu nasarori sosai gun yaki da ciwon zazabi maleria.

Zafafa Labarai