Countdown
Connect with us

Labarai

Elrufa’i ya jinjina ma shuwagabani unguwani da Jami’an tsaro kan tabatar da zaman lafiya a Kaduna

Published

on

Gwamna Jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufai. Hoto: insidekaduna Asali: Insidekaduna

Gwamna Jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufa’i, ya jinjina ma shuwagabani adina’i, na gargajiya, na unguwani tare da Jami’an tsaro na ganin jajircewa r su domin tabatar da wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar Kaduna.

Gwamna yayi jijina ne a wata sanarwa da yafitar a ranar talata, biyo bayan bitan sha’anin tsaro, duba da yada wasu jihohin Arewa ke zaman dardar bisa abubuwa dake faruwa.

Elrufa’i, ya tabatar da gamsuwar sa tayada wadanan mutane ke bada gudumawa don gani an samu zaman lafiya da tsaro a Jihar.

Gwamna, yayi kira ga iyaye da su tabatar da sun nunawa yayan su yin abubuwa na gari da bari abubuwan da zasu bude kofar da wasu zasu yi anfani dashi gun tayarda hankali al’umah.

Yakara da kiran jama’a da su rungumi girma ma adinan juna da kuma al’adu tare da kauracewa duk wani abu da zai ci mutunci adinan juna, sanan doka ita ce kadai hanyar ladaftar da mai laifi ba wai daukan doka a hanu ba.

Gwamnati Jihar Kaduna zata cigaba da aiki tare da Jami’an tsaro ta hanyar bibiyar lamura tare da hukunta masu son tayar da zauna tsaye a cikin al’umah.

Za kuma a hukunta duk wanda a ka samu Yana shirin kawo tashin hankali a Jihar Kaduna, komin mukamin sa.

Zafafa Labarai