Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

YANZU-YANZU: Elrufai ya bada hutu kwana uku domin ma’aikata suyi rigista katin zabe

Published

on

Gwamnati jihar Kaduna, karkashin jagoranci Gwamna Nasiru Elrufai, ta sanar da ranar laraba,alhamis da juma’a a matsayin ranukan hutu, domin ma’aikata suje suyi rigista katin zabe.

Bayani haka na kunshe ne a wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai ba ma gwamna shawara ka harkokin kafafen yada labarai, ya fitar a yau talata.

” Gwamna jihar Kaduna na rokon daukacin al’umar jihar da su fito suyi rigista katin zabe kafin ranar 31 ga watan Yuli 2022.

“Gwamna ya amince da ranar 27 zuwa 29 a matsayin ranakun hutu domin ba ma’aikata jihar damar da su samu su kamala rigista katin zaben su.

A wani labari kuma Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa ta tabatar dacewa ranar 31 ga watan Yuli, 2022 ne ranar da zata rufe rigista katin zabe.

Gwamnati Kaduna ita ma tabi ayarin takwarorin ta na wasu jihohi na ba ma’aikata hutu domin su kamala rigista katinan zaben su.

Zafafa Labarai