Countdown
Connect with us

Labarai

Elrufai ya amince da daukar Sabin malamai dubu goma

Published

on

Gwmana Elrufai na jihar Kaduna, ya amince ma hukumar malamai na bai daya KADSUBEB izini dauka sabin malamai dubu goma.

Tijani Abdullahi, ciyaman din hukumar ya sanar da haka a wata sanarwa da yafitar ranar juma’a a Kaduna.

Abdullahi ya ce shafin daukar aiki zai zai yi aiki na tsawon makwani 2 daga ranar 21 ga watan Yuli, 2022.

Kuma jami’ar Kaduna (KASU) ce za ta
hada shafin daukar aiki.

KARANTA: KDSG za ta kashe sama da #3bn gun daukar nauyin karatu dalibai a shekara 2022

Sanarwa ta bayana cewa “masu kwali NCE da kuma digiri a kowane bangare illimi daga jami’oi masu izini ne ke da damar nema gurbin aikin.”

Shafin zai yi aiki na tsawon mako biyu daga 21 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agosta, 2022.

“Akwai tsarin makaranta makaranta kowane mai shawa’awar nema zai zabi makaranta da tafi kusa dashi.”

“Za’a tantance dukan duk wanda ya nema aiki, wadan da sukayi nasara ne kawai za agayata don rubuta jarabawa a matsayin mataki na gaba.

Za a gudanar da jarabawa a gurare uku da suka hada da Kaduna, Kafanchan da Zaria.”

“Wadan da sukayi samu nasara maki daga kaso 75 zuwa sama ne kadai za’a gayata zuwa tantancewar na gaba.

“Kuma za abukace wadan da sukayi nasara su zo da takardun su na asali da fotokofi, inda za a duba takardun tare da karbar fotokofi din.”

Daukar aikin na zuwa ne satituka bayan korar malamai sama da dubu biyu bisa faduwa jarabawa chanchanta da a ka gudanar musu.

Zafafa Labarai