Countdown
Connect with us

Labarai

El-Rufai ya sauya sunayen wasu gine-ginen, hanyoyi don karama mutane da sukayi wa jihar hidima

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta sauya sunayen wa wasu gine-gine da tituna domin karrama mutanen da suka yi wa jihar hidima da Najeriya .

Da yake kaddamar da sunayen, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce: “Gwamnatin jihar ta fara aiwatar da aikin sanya sunayen tituna tun daga shekarar 2015 a matsayin muhimmin abin da zai taimaka wajen tsara garuruwan mu.

“Ayyukan da aka gudanar a matsayin wani bangare na shirin sabunta birane sun kara kaimi wajen samun karin sakamako a wannan fanni. Dama ce ta karrama wadanda suka yi wa wannan jiha hidima, ko kasarmu ko kuma alumah baki daya.

“ Girmama wadanda suka yi aiki wajibi ne kowane sashe na shugabanni da ke bin wadanda suka zo a baya.

Wannan atisayen, in ji shi, kuma wata dama ce ta mutunta tarihi da kuma fayyace sunayen tituna.

“A yanzu an amince da hidimar Sir Kashim Ibrahim tare da canza sunan duk fadin titin Sokoto don karrama shi.

“Daga yanzu hanyar da ta kai gidan Sir Kashim Ibrahim (Gwamnati) za a rika kiranta da Sir Kashim Ibrahim Road.

An sauya sunan gidan saka hannun jarin ne don karrama tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo yayin da aka sanya sunan harabar babbar kotun jihar don girmama mai shari’a Muhammadu Lawal Uwais, tsohon babban jojin Najeriya (CJN).

An canza sunan Sakatariyar Jiha ne don girmama Maccido Dalhat, tsohon SSG.

An canza sunan Hukumar Kula da Kayayyakin Gwamnati ta Jihar Kaduna (KADPPA) don karrama Architect Barnabas Yusuf Bala, wanda ya zama Mataimakin Gwamna daga 2015 zuwa 2019.

An ba wa rukunin Ma’aikatar Lafiya suna bayan Dorathy Miller, Kwamishinan Lafiya mafi dadewa.

An canza wa ginin Hukumar Babban Birnin Kaduna suna don girmama Magajin Gari Sambo.

College Road Ungwan Dosa, bayan AVM Usman Muazu, tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna.

Zafafa Labarai