Countdown
Connect with us

Rahotoni

YAJIN AIKI: Duk da alkawari da Gwamnati Jihar Kaduna tayi wa daliban Jami’ar Kaduna, wata 3 kenan ana yajin aiki

Published

on


Gwamnati Jihar Kaduna, karkashin jagoranci Elrufai, bata cika alkawari da tayi wa daliban Jami’ar Kaduna (KASU), Kan maganar yajin aiki…..

Kimanin wata uku kenan Jami’ar Kaduna (KASU), na kan yajin aiki dake gudana a kasa baki daya….

Kofar shiga Jami’ar Kaduna KASU

A ranar 1 ga watan June, shekara 2021 lokacin da daliban jami’ar Kaduna ke gudanar da zanga-zanga Kan batun Karin kudin makaranta da Gwamnati Jiha tayi a dukan makarantu gaba da sakondari.

Dalibai yayin gudanar da zanga-zanga, sunyi kokarin kawo kukan su gidan Gwamnati a wanan ranar, ama Jami’an tsaro ‘yan sanda da kuma civilian JTF ba su bar su sun karasa kofar gidan Gwamnati ba.

Sai dai sun dauki wasu daga cikin dalibai domin wakilta sauran daliban gun isar da sakon su ga Gwamnati Jihar Kaduna.

Wakilan dalibai Jami’ar Kaduna, sun samu damar zantawa da Gwamnati Jihar Kaduna wace Mataimakiyar Gwamna Dr. Hadiza Sabuwa Balaraba, ta jagoranta kan batun Karin kudin makaranta.

A yayin jawabin sa Malam Balarabe Abbas, Sakataren Gwamnati, bayan jin korafin dalibai, yace,

Gwamnati Jihar Kaduna na son samar wada dalibai garanti ne tayada duk wanda yasamu gurbin karatun a jami’ar na tsawon shekara hudu to a shekara hudu zai gama haka zalika masu karatu shekara biyar ko sama da haka.”

https://www.facebook.com/nasirelrufai/videos/1126955117825633/?app=fbl

Kamar yadda yake cikin video da Gwamnati Jihar ta walafa a shafukan ta na sadarwa a ranar 3 ga watan June, din 2021.”

DANA NAN DOMIN KALON VIDEO TATTAUNAWA

Duk da karin baiyi wa daliban dadi ba haka nan suka hakura, tare da taimakon tsarikan da Gwamnati da hukumar makarantar ta samar domin sauqa qa hanyar biyan kudin makarantar.

Yau kimani wata uku rak daliban Jami’ar na gida sabida yajin aiki da ake gudanarwa wanda ya saba alkawari da Gwamnati Jihar Kaduna tayi musu.

Duk da hukumar makarantar ta sanarda dawo wa makaranta ama kungiyar Malamai rashen Jami’ar (ASUU-KASU), suki bada hadin kai.

Jaridar Kadunareporters, ta zanta da wani dalibi da ya bukaci a sakaya sunan sa inda yace ” Gaskiya Gwamnati Jihar Kaduna, ba ta kyauta ba kuma bai kamata ace takasa cika alkawari da ta dauka ba, Mu dalibai mun cika namu domin mun amince da dukan sharudan da suka gindaya mana.”

Wata dalibi Yar ajin karshe ta bayana cewa, wata kila don ba kowa yabiya duka kudin makaranta sa ba gaba daya, ta yu shiyasa Gwamnati Jihar bata sa baki ba.

Saidai wani sabon dalibi yace, ” shi Kira zaiyi ga Gwamnati Jihar domin ta taimaka ta cika alkawar da tayi, domin alkawari ne ya karfafa mai gwiwa yin karatu a Jami’ar.

Zafafa Labarai