Countdown
Connect with us

Tsaro

Daya Daga Cikin Mata Masu Ciki Da Aka Sace A Jirgin Kasa Zuwa Kaduna Ta Haihu A Hanu Yan Bindiga

Published

on

Daya daga cikin mata biyu masu juna biyu cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a watan da ya gabata ta haihu, kamar yadda jaridar THISDAY ta samu a daren jiya.

Haka zalika, ‘yan ta’addan da suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjojin sun fitar da hotuna daban-daban guda hudu na wadanda abin ya shafa, adadinsu ya kai 62.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka yi wa jirgin kasan da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga babban birnin kasar kwanton bauna bayan da suka tada bam a hanyar jirgin kasa.

Tashar Talabijin ta ARISE , reshen watsa labarai na THISDAY, ta nakalto ‘yan kungiyar suna dagewa cewa ba wai suna bukatar a biya su kudin fansa ba ne, amma suna so ayi musayar fasinjojin da suka sace tare da kwamandojinsu da ake zargin suna hannun gwamnati ne.

An kashe mutane tara, ciki har da wani matashiyar likita a yayin harin, an kuma jikkata wasu da dama tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji sama da 62.

Tashar Talabijin ta kara da cewa wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa daya daga cikin mata biyu masu juna biyu da aka yi garkuwa da su, ta haihu a kogon ‘yan ta’addan tare da taimakon likitocin da ‘yan kungiyar suka gayyato.

Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addar suna da tsari da kuma hada kai domin yadda ‘yan ta’addan ke samun kayayyakin jinya a cikin dajin, al’amarin da suka bayyana a matsayin har yanzu yana da matukar tayar da hankali ga jami’an gwamnati da na tsaro.

Hotuna guda hudu da ‘yan ta’addan suka fitar kuma THISDAY suka gani sun nuna wadanda aka sace a kungiyoyi hudu, na farko sun nuna mutane 23 da suka hada da yara biyar da mata 18.

A cikin hoto na biyu, an ga mutane 17, ciki har da wani mutum mai kama da dan Indiya, yayin da hoto na uku ya nuna shida daga cikin wadanda abin ya shafa a zaune, tare da bandeji a nannade a daya daga cikin kafar dama ta wanda abin ya shafa. Hoto na hudu ya nuna wani rukuni na mutane 16 a zaune.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan ta’addan sun fitar da wani faifan bidiyo kimanin mako guda da kai harin, wanda ke nuna lokacin da suke shirin sakin Manajan Daraktan Bankin noma, Alwan Ali-Hassan ga iyalansa.

THISDAY ta kuma tattaro cewa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su sun kuma rubutawa mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Maj.-Gen. Mohammed Munguno (rtd), don neman a basu rahoto kan halin da ‘yan uwansu ke ciki.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Afrilu mai dauke da sa hannun Aliyu Mahmood da Idayat Yusuf da Aminu Othman da Dokta Baaba Muhammed a madadin iyalan wadanda abin ya shafa, sun koka da cewa hukumomi sun bar su cikin duhu.

Mu, iyalan wadanda harin jirgin kasan Najeriya ya rutsa da su a jirgin kasan Ak9 da ya taso daga Abuja ranar 28 ga Maris, 2022 zuwa Rigasa Kaduna, mun taru a madadin wadanda aka yi garkuwa da su.

“Mun rubuto ne don nuna damuwarmu cewa babu wata wakilci daga gwamnati da ta yi magana da mu kan matsayin ‘yan uwanmu . Ko da yake mun san bayanin na iya zama na yanayin sirri, amma duk da haka, iyalai suna buƙatar ƙarfafawa kuma a ɗauke matakai cikin aminci don tabbatar da sakinsu daga hanun wanda sukayi garkuwa dasu.

“Muna rokon taimakon ku don tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na tuntubar iyalan wadanda abin ya shafa. Mun gode,” cewar wasikar.

Sai dai wata majiya mai tushe ta ruwaito cewa mata masu juna biyu da ke cikin fasinjojin jirgin da aka yi garkuwa da su, a cewar Arise, ta haihu a karshen mako.

Matar da aka ruwaito tana dauke da ciki wata takwas a lokacin da aka kai harin, ta haihu lafiya bayan an ce ‘yan ta’addan sun gayyaci jami’an kiwon lafiya domin zuwa wurinta. Sai dai ba a san halin lafiyar ta da jaririn ba.

“A cewar rahotanni daga majiyoyin ‘yan uwa, ta haihu ne da taimakon likitocin da ‘yan ta’addan suka kawo. Za mu kuma iya cewa ‘yan ta’addar na neman a sako manyan kwamandojin su a madadin fasinjojin jirgin da aka sace.

“A cewar majiyoyi, ‘yan ta’addar suna magana ne da yaren Kanuri, Wanda yake nuna cewa sun fito ne daga yankin arewa maso gabas kuma suna samun goyon bayan kungiyar Islamic State-ISWAP,” in ji rahoton Arise.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa gwamnati na fargabar cewa fursunonin da ke da alaka da Boko Haram idan aka sake su za su iya haifar da babbar barazana ta tsaro ga al’ummar kasar.

A yau ne ake sa ran iyalan wadanda aka yi garkuwa da su za su gudanar da taron manema labarai a Abuja da Kaduna domin kara matsa lamba ga gwamnati ta ceto ‘yan uwansu da aka Yi garkuwa da su.

An ruwaito wani masani kan harkokin tsaro, Abubakar Ahmed, yana cewa, sakon da ke kunshe cikin sakin hotunan, ya bayyana cewa, “Suna so su shaida wa duniya cewa fasinjojin da aka sace suna nan a raye kuma suna cikin koshin lafiya.”

Wata majiya daga cikin iyali wanda akayi garkuwa dasu ta kara da cewa: “Wace irin kasa ce muke rayuwa a ciki? Da alama babu wani abu a cikin labarai. Shin gwamnati ma tana yin wani abu a kai ko ta’addanci yanzu ya zama wani bangare na al’ada da al’adunmu?

“Sonny Okosun ta wace hanya ce Najeriya ta kasance a 1984. Kusan shekaru 40 bayan haka, har yanzu muna yin irin wannan tambaya.”

Wani dangin daya daga cikin wadanda abin ya shafa, ya yi ikirarin cewa sun damu tun lokacin da hotunan suka fito, yana mai jaddada cewa: “Mun kasance muna yi masa addu’a da sauran mutane dare da rana.”

THISDAY ta ci gaba da samun labarin cewa wasu tsofaffin da abin ya shafa sun koka da tabarbarewar lafiyarsu.

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira miliyan 18 ga iyalan mutane tara da aka kashe a harin, inda ta ce ba diyya ba ne, illa dai wani tallafi ne.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Mista Muhammed Mukaddas, ya bayyana cewa Gwamnan ya kuma amince da raba Naira 250,000 kowannensu ga mutane 22 da suka samu munanan raunuka a harin jirgin kasa.

Source and photo credit: Thisdaylive

Zafafa Labarai