Countdown
Connect with us

Illimi

Dawowa Makaranta Na Nan Daram Ranar 9 Ga Watan Mayu – Mahukuntan Jami’ar Kaduna

Published

on

Kofar shiga jami’ar Jihar kaduna

Duk Da Iqirarin Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar kaduna (ASUU-KASU), na kin amincewa da batun komawa karatu a Jami’ar Jihar kaduna (KASU), a ranar 9 ga watan Mayu, 2022.

Hukumar Makarantar ta kara jadda cewa batun komawa makaranta na nan daram a ranar 9 ga watan mayu, 2022.

In za a tuna ranar 27 ga watan Afrilu, 2022 ne hukumar Jami’ar ta fitar da sanarwa cewa tana umurtan dukan dalibai da Malamai da su dawo bakin karatu a ranar 9 ga watan mayu, 2022.

Wanda hakan baiyi wa Kungiyar Malaman jami’ar dadi ba, inda suka musanta batun tare da cewa suna Kan yajin aiki kuma ba zasu dawo ba har sai ranar da aka janye yajin aikin da ake kai baki daya, a wata sanarwa da Suka fitar a ranar 3 ga watan mayu, 2022.

Kwatsam ranar 6 ga watan mayu sai ga wata sanarwa daga jami’i Mai kula da hulda da jama’a na Jami’ar, Nuhu Adamu Bargo, inda ya kara bada tabacin cewa batun komawa makaranta na nan daram ranar 9 ga watan mayu, 2022.

Ya Kuma umarci dukan dalibai da su dawo makarata don cigaba da karatun su, ya Kara dacewa, ba zasu laminci a wani togaciya ba da ga gurin kowaye Kan batun dawo wa karatu.

Za Kuma mu sanar da daukacin al’uma kan sabon sauyi in har an samu .

Zafafa Labarai