Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Datti Baba-Ahmed ya Janye daga takara kujera Gwamna Jihar Kaduna

Published

on

Sen. Yusuf Datti Baba-Ahmed

Dan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna, a inuwar jam’iyar PDP a Kaduna, Sen. Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya janye daga takara neman kujera Gwamna awa 24 kafin zaben fidda gwani.

A ranar laraba ake sa rai za a gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnoni a jam’iyar PDP, a Kaduna, akwai tsohon Gwamna Ramalan Yero, tsohon Sanata Shehu Sani, tsohon dan Majalisa Ashiru Kudan da ma wasu, wanda zasu fafata a zaben.

Sai dai kuma a wata takarda da Baba-Ahmed ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Mista Hassan Hyet a Kaduna, ya ce har yanzu jam’iyar PDP ba ta koya darasi ba.

Ya ce, “wadannan sun saba da manufar kasancewata a siyasa.”

Baba-Ahmed wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Arewa a shekarar 2011 zuwa 2012 ya ki bayar da takamammen dalilin da ya sa ya janye a takara ba amma ya jaddada cewa zai ci gaba da biyayya ga jam’iyyar PDP.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Baba-Ahmed, ya jaddada cewa idan ba a bincika abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar PDP na iya yin illa ga damarta a 2023.

“Saboda haka na fice daga takarar gwamna a jihar Kaduna cikin girmamawa a 2023 a karkashin babbar jam’iyyar mu ta PDP. Ni duk da haka, na kasance da aminci da goyon baya. Ina addu’ar ranar da za mu gyara siyasarmu saboda Najeriya,” inji shi.

Rohotoni daga wakilin jairidar Daily Trust na bayana cewa, siyasar kudi ne yasanya Baba-Ahmed, janye wa duba da yadda abubuwa suka faru a yayin zaben fidda gwani na Yan Majalisu, a jam’iyar PDP.

Zafafa Labarai