Countdown
Connect with us

Tsaro

Dan yi ma kasa hidima ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindiga a hanyar Abuja

Published

on

Batachan harsashi yayi sanadiyar mutuwar mai yi wa kasa hidima (NYSC), a yayin a rangama tsakanin Jami’an tsaro da’yan bindiga a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Jaridar daily Post ta rawaito cewa, a rangamar ta afku ne da misalin karfe 8 na daren ranar juma’a, daidai lokacin da ‘yan bidingar ke kokarin tsalako kan baban hanyar kwauyen Kasarami, dake kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Mamacin wanda yake yi wa kasa hidima a baban birnin taraya Abuja, ya rasa ransa sanadiyar batacen harsashin da ya sa me shi a kai, daidai lokacin da yake cikin moton haya zuwa Kaduna.

Wani jami’in dan sanda wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, sabida bashi ne ke da alhakin bayana a bun da yafaru ba ya ce, a kala akanshe ‘yan bindiga guda bakwai a yayin artabun.

” Ya ce batachan harsashi ne yayi sanadiyar mutuwar mamacin, sabida zazafar musayar wutan da ya afku a tsakanin ‘yan bindiga da kuma jami’an tsaro daidai lokacin da suke kokarin tsalakowa kan titin kauyen Kasarami, cewar jami’in.

Jami’an tsaro ciki harda sojojin dake Rijana, ne suka dakile ‘yan bindigar, tare da kashe 7 da Kwato wasu mashina.

Yace an garzaya da mamacin asibitin St. Gerald dake Kakuri, cikin birnin Kaduna, inda likitoci suka tabatar da mutuwar sa.

Saidai ba a iya jinta bakin Jami’i Mai kula da hulda da jama’a na Rudunar Yan Sanda Jihar kaduna, ASP Mohammed Jalinge, ba yayin hada rahoton.

Zafafa Labarai