Countdown
Connect with us

Labarai

Dalilan daya sa muka mayar da Investment house zuwa sunan Namadi Sambo – Elrufai

Published

on

Namadi Sambo, ya bada gudun mawa sosai a jihar Kaduna, ya kadamar da tsare tsare na Kawo cigaba a Jihar. In ji Elrufai.

Gwmana jihar Kaduna, Nasiru Elrufai ya bayana dalilin dayasa aka maida investment house zuwa sunan tsohon mataimaki Shugaban kasa Namadi Sambo.

Elrufai ya bayana hakan ne a lokacin fira ta musaman a kafatanin gidajen radio jihar a makon.

“Mun sani Namadi Sambo ya kawo tsare tsare cigaba sosai a jihar Kaduna, wanda Allah Bai bashi iko ba sabida ya zama mataimaki Shugaban kasa.” cewar Elrufai.

“Babu wanda yakai Namadi Sambo mukamin Gwamnati a fadin jihar Kaduna, a tarihin Jihar Kaduna shine kadai wanda Allah ya dauka ka har yakai matsayin mataimaki Shugaban kasa.”

Namadi Sambo, yayi Gwamna a Kaduna inda ga bisani ya tafi mataimaki Shugaban kasa bayan rasuwar Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.

Zafafa Labarai