Countdown
Connect with us

Illimi

Daliban kwalejin Illimi Gidan Waya, Sun koka Kan rashin igantace muhali karatu

Published

on

daya daga cikin gini a kwalejin illimi Gidan waya Hoto: Kadunapoliticalaffairs Asali: Kadunapoliticalaffairs

Kungiyar dalibai Jihar Kaduna rashen kwalejin Illimi Gidan Waya, dake Jihar Kaduna sun koka Kan rashin ingantacen muhali da kwalejin ke fama dashi.

Bayanin hakan na kunshe ne a wani takarda da suka tura ma Jaridar Kaduna Political Affairs, a ranar asabar.

Daliban sunyi kira ga Gwamna Jihar Kaduna, Kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs), tsofafi daliban makarantar da su kawo musu agaji gun gyaran makaranta.

Duk da makudan kudaden da daliban kwalejin ke biya a matsayin kundin makaranta, kwalejin bata da hanyoyi masu kyau, Kuma acike take da gine gine da ba akarasa ba. Inji su.

Hoton daya daga ciki hanya a Kwalejin Illimi Gidan Waya Hoto: Kadunapoliticalaffairs Asali: Kadunapoliticalaffairs

Cikin korafin da suka gabatar sun hada da, rashin ingantacen dakunan kwanar dalibai, dakin bincike, karanci kayan aikin sadarwa na zamani, ka ranci litatafen karatu a dakin karatu, hanyoyi da sauran su.

Takarda Koken ta samu sa hanu shugaban kungiyar dalibai Jihar Kaduna reshan kwalejin, Danladi Louis Ninyio.

Zafafa Labarai