Countdown
Connect with us

Labarai

Dalibai daga makarantu 15 suka samu damar halata fareti bikin ranar yara ta duniya a kaduna

Published

on

Gwamnatin Kaduna tayi murna bikin Yara na duniya tare da cikar jihar shekarar 55 da kafuwa.

Dalibai makaratu a dandalin Murtala lokacin bikin Yara ta duniya a kaduna. Hoto: The Governor Of Kaduna State. Asali: Facebook.

A qalla daliban makarantu firamare da sekondiri 15 ne daga fadin jihar kaduna ne suka samu damar halarta fareti bikin ranar yara ta duniya, wanda ya gudana a dandalin Murtala dake birnin Kaduna.

Tare da farinciki cikar jihar shekara 55 da samuwa, an dai kafa jihar Kaduna ne a ranar 27 ga watan Mayu, 1967.

A yayin jawabin sa Gwamna Elrufai, Kan kokarin Gwamnatin Jihar Kaduna kan yaran jihar, yace ” a yayin da yaran mu ke zama matasa masu tasowa, lalai suna bukatar aiyukanyi da yanayi da zai basu damar bage fasahar su ta kirkire kirkire da kasuwanci. Shiyasa Gwamnatin Jihar ke kokari gurin samar da masu zuba hanu jari a fadin jihar, tayada zasu samar da aiyukan da yayan mu suke bukata tare da bunkasa fasahohin su.”

Mahalarta bikin sun hada da Mataimakiyar Gwamna Jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balaraba, Mambobin Kaduna Executive Council, dalibai, Malamai dakuma bakin da aka gayata.

Gwamnatin Kaduna ta yaba da kokarin da Malamai da dalibai sukayi nagani an kamala fareti bikin cikin nasara.

Zafafa Labarai