Countdown
Connect with us

Labarai

Dakaru Sojoji sunyi nasara fatatakan ‘yan bindiga a Kaduna

Published

on

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya, ta sanar da rahotonin fatatakan’yan bindiga a wani atisaye da ta gudanar a jihar Kaduna.

Atisayen wanda yayi sanadiyar kama ‘yan bindiga uku tare da kashe daya a musayar wuta.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Birgediya Janar, Onyema Nwachukun, jami’i mai kuka da hulda da jama’a na rudunar sojin kasa ya fitar a yau talata.

Sanawar ta bayana cewa, a wani atisaye na fatatakar ‘yan bindiga da GOC hedikwatar rundunar soji ta daya (1Div), Mejo Genar Taoreed Lagbaja, ya jagoran ta tare da jami’an tsaron, sunyi nasarar fatatakar ‘yan bindiga a yankuna Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello and Dogon Dawa jihar Kaduna.

Atisayen wanda ya gudana a ranar litini 29 ga watan Agusta, 2022 yayi nasara chafke mutum uku tare da kashe date a yayin zazzafar musayar wuta.

Bugu da kari, sojojin sunyi nasara kwato bindiga kirar AK47 guda daya da alburushi kirar 7.62mm guda 27 tare da babura 18.

Sai dai sanarwa ta jawon hankalin asibitoci domin sa ido domin wasu daga cikin ‘yan bindiga sun tsira da raunuka harbi a jikin su, da kuma su sanar da Jami’an tsaro cikin gaggawa.

Zafafa Labarai