Countdown
Connect with us

Wasanni

Cinikaya: Chelsea da Leicester sun cin ma yarjejeniya akan Wesley Fofana

Published

on

Kungiyar kwalon kafa ta Chelsea ta cinma yarjejeniyar da kungiyar Leicester akan Dan wasa baya Wasley Fafona.

Jaridar The Team ta rawaito cewa, an cima yarjejeniyar ne akan kudi yuro miliyan 82.5 wanda in hakan yatabata Fafona zai zamo Dan wasan baya mafi tsada a tarihi.

Fafona Mai shekara 21 na shirin dawo wa kungiyar wasan kwalon kafa ta Chelsea, inda ake sa rai za rataba hanu akan kwantiragi har zuwa kakar shekara 2027.

Rahotani sun bayana cewa a ranar Juma’a ne dai kungiyar kwalon kafa ta chelsea ta chin ma yarjejeniya tsakanin ta da kungiyar Leicester akan dan wasan.

In komai ya tafi daidai, Fafona zai zama dan Wasa baya mafi tsada domin zai zarce Harry Maguire wanda kungiyar Leicester ta siyar a shekarar 2019.

Zafafa Labarai