Countdown
Connect with us

Illimi

Buhari ya nada Dr Suleiman Umar Rector din KADPOLY

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Suleiman Umar a matsayin shugaban kwalejin fasaha ta Kaduna.

Nadin zai fara aiki nan da nan daga ranar 27 ga Yuni, 2022 kuma na tsawon shekaru biyar ne.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin magatakardar yada labarai da ka’ida Samuel Y. Obochi, wanda ya rabawa Aminiya.

Dr Suleiman ya fito ne daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu a jihar Kaduna.

Ya yi digirin digirgir (Ph.D) a fannin ilmin lissafi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kwararren memba ne na kungiyar ilimin lissafi ta Najeriya (MAN).

Ya yi aiki a matsayin shugaban sashen, lissafi da kididdiga, da tsare-tsare na ilimi da mataimakin shugaban gudanarwa a Polytechnic.

Har zuwa lokacin da aka nada shi, Dr Suleiman ya kasance shugaban riko na makaranta.

Zafafa Labarai