Countdown
Connect with us

Tsaro

Bayan sace amarya mai ciki, ‘yan bindiga sun kashe angonta a kaduna

Published

on

‘Yan bindiga sun kashe sabon ango tare da sace amarya sa Mai dauke da juna biyu a garin Jere dake karamar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Jaridar dailyTrust ta rawaito cewa, ‘yan bindiga sun sace harda iyalai hudu na tsohon Kwamishina rage radadin taulaci na jihar Kaduna, Abdulrahman Ibrahim Jere.

Dailytrust ta tattauro cewa a qalla ‘yan bindiga 50 ne a kan babura suka far ma garin Jere dake kan titi Abuja, inda suka rika shiga gida gida, saidai mazauna garin sunce kamar dai gidan Tsohon Kwamishina Abdulrahman Ibrahim Jere suka zo, kuma bama ya gari a lokaci.

Sunyi nasara garkuwa da matarsa, karamar yarinya, kanwar sa da kanwar matan sa.

Hassan Adamu Jere, wani ma zauni garin, ya Kara da cewa ‘yan bindiga sun shiga gidan wani sabon ango inda sukayi kokarin garkuwa da amarya sa, ama angon yayi yunkuri hana su.

Yayin kokarin kubutar da amarya sa, ‘yan bindiga suka harbe shi nan take.

A qalla ‘yan bindiga sun kwashi sa’oi uku suna gudanar da ayukan su ama Jami’an tsoran dake girke yanki ba su kawo dauki ba.

“Duk da mun ta kiraye kiraye ga Jami’an tsoran da ke gurin ama basu kawo mana dauki ba, wanan shine mumuna hari na biyu da ‘yan bindiga su ka kawo garin Jere a cikin watanin uku, muna ji Jami’an tsoran dake yanki basu da anfani kwatakwata a gun mu cewar matashi Adamu, cikin fushi.”

Ibrahim Salisu, shima yakara dacewa zamu shigar da kara Kan Jami’an tsoran da aka girke a garin Jere, domin yadda suke yi kai kace ” kodai sun hada Baki da ‘yan bindiga ko kuma basu da mu da tsaron rayukan al’umar mu ba.”

A cewar sa, Sa’oi bayan ‘yan bindiga sun tsere ne Jami’an tsoran sukayi yun kurin bin bayan su, inda suka dawo Suka fada Yan gari cewa sunyi nasara kashe ‘yan bindiga biyu.

Jami’i Mai Kula da Hulda da Jama’a, na Rudunar ‘Yan Sanda Jihar kaduna, ASP Mohammed Jalinge, bai amsa kira da aka masa domin neman karin bayani yayin hada wanan rahoton.

Zafafa Labarai