Countdown
Connect with us

Labarai

BARKA DA SALLAH: Mr. La yaraba raguna 450 ga al’umar Kaduna ta tsakiya

Published

on

Dan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a PDP Hon. Lawal Adamu Usman ya raba raguna sama da 450 a fadin yankin Kaduna ta tsakiya domin baiwa al’ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki na wannan shekarar.

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun hada da Shugabannin Jam’iyya da masu ruwa da tsaki, ‘yan majalisar yakin neman zabe, kungiyoyin addinai, malaman addini da kungiyoyi na shiyyar.

Dan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya na jam’iyyar PDP ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kaduna da ma kasa baki daya.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ware ranakun Litinin, 11 ga watan Yuli da Talata, 12 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan sadaukarwa na bana.

Kamar yadda yake yiwa daukacin al’ummar musulmi barka da Sallah da Hajj Mabroor .

Zafafa Labarai