Countdown
Connect with us

Siyasa

Ban yadda da tsaida Uba Sani da Elrufai yayi a matsayin dan takara Gwamna Ba – Hon. Sha’aban

Published

on

Hon. Sani Sha’aban

Yayin da zaben shekarar 2023 ke ta karatowa a Nijeriya, Kamar yadda kundin tsarin mulki kasa ya ta nada duk bayyan karshen wa’adi to a gudanar da zabe.

Yan siyasa na cigaba da fito wo da nuna bukatun su na son darewa karagar mulki kujeru daban daban, a fadin Nijeriya tundaga kan kujerar shugaban kasa, gwamna, Yan majalisu jiha da na taraya da sauran su.

A kaduna rikici na son kunawo a jam’iyar APC mai mulki, yayin da Elrufai ya amince da Sanata Uba Sani, a matsayin dan takarar gwamna da zai gwabza a zabe 2023 a inuwar jam’iyyar APC a Kaduna.

Sai dai, wasu daga cikin abokan karawar Uba Sani, a jam’iyar APC na ganin hakan sam bai dace ba kuma ya ci karo da tsarin dimokradiyya.

Daya daga cikin Dan takarar gwamna jihar kaduna a jam’iyar APC, Hon. Mohammed Sani Sha’aban, ya ki amincewa da Sanata Uba Sani, a matsayin dan takara Gwamna, Wanda Elrufai, da wasu jiga jigan jam’iyyar APC su ka amince ama tsayin dan takara Gwamna a Kaduna.

Sha’aban ya bayana zabin a matsayin saba tsarin dimokradiyya, inda yace kaso casa’in (90%), na mambobi da Kuma ma su ruwa da tsakin jam’iyar APC a kaduna basu amince da hakan ba.

Sha’aban wanda tsohon dan takarar gwamna jihar ne a jam’iyar ANPP a zaben 2007, kuma tsohon dan takarar gwamna a jam’iyar AAC a shekarar 2011, yace da shi da magoya bayan sa ba za su amince da ko wane kalan zabi ba in dai ba zaben fidda gwani ba.

Yayin ganawa da mane ma labarai, Sha’aban, yace ya samu labari tsayar da gwaman Elrufai, yayi ma sanata Uba Sani a matsayin dan ta kara jam’iyar APC ne, batare da an tuntube shi ba a matsayin sa na mamba jam’iyar APC, kuma dan takarar da yafara siyan fom din neman kujerar gwamna jihar kaduna a jam’iyar APC.

Hakan ya saba wa tsarin mulki dimokradiyya, kuma ba za su lamunta hakan ba, ya Kara dacewa yin hakan tamkar zagi ne a gare shi.

Zafafa Labarai