Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Babu delegates din da zan ba ko ficika Kuma bana so wani ya ba su a ma dadi na domin su zabe ni – Shehu Sani

Published

on

Sen. Shehu Sani Hoto: Shehu Sani Asali: Twitter

Dan takarar kujerar Gwamna Jihar Kaduna, a inuwar jam’iyyar PDP, Sen. Shehu Sani, ya ce babu delegates din da zai ba wa ko ficika domin ya zabe shi a zaben fidda gwani, Kuma bai amince wani ya bawa delegates din kudi ba domin su zabe shi.

Shehu, ya bayana hakan ne jim kadan bayan janyewar takara da Datti Baba-Ahmed, da yayi a jiya talata, a shafin sa na Twitter.

” Zaben fidda gwani na takara Gwamna Jihar Kaduna; ba zan biya kowani delegates ba damin su zabe ni Kuma kada wani ya biya su domin su zabe ni. Ina maraba ne dukan kuri’u da min kyaukyauwar manufata akan mutane Jihar Kaduna. Ba zamu gina ko ciyar da kasar mu gaba ba ta hanyar zabi mara kyau.”

Sen. Shehu Sani, shine tsohon Sanata Kaduna ta zakiya a shekara 2015 zuwa 2019, kuma dan takara Gwamna Kaduna a jam’iyar PRP a shekara 2019, yan zu kuma dan ta kara Gwamna Kaduna a jam’iyar PDP.

Zafafa Labarai