Countdown
Connect with us

Labarai

Babu barazanar da zata sa mu janye yajin aiki, martani ASUU-KASU ga hukumar jami’ar Kaduna

Published

on

Kungiyar malaman jami’a rashen jami’ar Kaduna (KASU), tace babu wata barazana da zatasa su janye yajin aiki da suke yi.

Peter Adamu, shugaban kungiyar rashen jami’ar Kaduna ne ya bayana haka a ranar talata, lokacin da yake ganawa da mane ma labarai a Kaduna.

A ranar litini data gabata ne dai hukumar makaranta ta fitar da sanarwa cewa tana umurta malamai jami’ar da ke yajin aiki su dakatar da yajin aiki, ko kuma su fuskanci hukunci.

Ana sa martani Adamu, yace hata dokar cikin kasa da na ketare ta amince da yajin aiki, musaman yajin aiki irin wanan da akeyi.

Ya kara da cewa ” Babu wata sashin doka a Jami’ar Kaduna ko na ma’aikata data yi nuni kan hukunta malamai dake yajin aiki kan abin da zai kawo cigaba a jami’ar.”

Kundin tsarin mulki na kasa wanda shine mafi kololuwa a gun doko yayi tanadi kan amincewa da yajin aiki. A cewar sa.

Yajin aikin da ake gudanar wa domin kawo cigaba ne a jami’oin Nijeriya, ciki harda jami’ar Kaduna, ku zagaya cikin harabar jami’ar mafi yawa daga gine-gine jami’ar Kaduna, horar da malamai da sauransu sun samu ne a dalilin kalar wanan yajin aiki.

Adamu yace babu wata barazana da zata yi tasiri a gun malamai dake ASUU, an samu barazana dayawa a lokacin mulkin soja ama kotu tayi wancha kali dasu.

Yatabatar da cewa Basu janye yajin aikin ba, kuma suna nan daram, har sai Gwamnati taraya tayi abinda yakamata.

Akarshe yayi kira ga gwamnati jihar da dalibai da su fahimci cewa lamari irin wanan yana faruwa ne domin ceto jami’oi daga rushe wa.

Zafafa Labarai