Countdown
Connect with us

Da Dumi Dumin Sa

Ba Za Mu Lamunce Zanga Zangar Addini’ Ba, Kuma Zamu Hunkata Duk Wanda Ya Aikata A Kaduna – Elrufa’i

Published

on

Gwamna Jihar kaduna, Nasiru Elrufai

Gwamnatin Jihar kaduna, ta haramta duk wata nau’in zanga zanga addini’ a fadin jihar.

Kuma gwamnatin za ta hukunta duk wanda takama da aikatawa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishina tsaro da harkokin cikin gida jihar, Samuel Aruwan, ya fitar a yau sati 14 ga watan mayu, 2022.

Sanarwa ta bayana cewa ” biyo bayan tattaunawa da Jami’an tsaro, a karkashin inuwar Kaduna State Security Council, gwamnatin Jihar kaduna ta haramta duk wani nau’in zanga zanga addini’ a fadin jihar baki daya.

Gwamna Elrufai, ya baiwa Jami’an tsaro umarni tsaurara matakai gun gani sun tabatar da dokar a dukan lungu da sakon Jihar.

Elrufai, yayi kira ga shuwagabanin unguwani, sarakuna, malamai addinai da su tabatar da sun ba da hadin kai kan kokari da gwamnati da Jami’an tsaro sukeyi gun wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar.

A don haka, Jami’an tsaro zasu dakile duk wani yunkuri wani ko wasu kungiya da zasu kawo cikas ga zaman lafiya a fadin jihar, ta hanyar zanga zangar addini’, tare da hukunta duk wanda aka kama gun aikata hakan.

Zafafa Labarai