Countdown
Connect with us

Illimi

Jami’ar Jihar Kaduna Ta Sanya Ranar Komawa Makarata

Published

on

Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta fitar da sanarwa ciga ba da karatu zango na biyu na shekarar karatun 2020/2021.

Bayanin hakan na kunshe be a wani sanarwa da ya fito daga ofishin rigistara Jami’ar dauke da sa hanun sakataren ilimi jami’ar, Abdullahi Zubairu, Esq.

Inda sanarwa ka dauke da bayani Kamar haka:

“An umurce ni da in sanar da dukkan ma’aikata da dalibai cewa jami’ar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na ilimi a zango na biyu na shekarar 2020/2021 a ranar 9 ga Mayu, 2022. Don haka ana ba ku shawara ku bi kalandar ilimi.

Ina yi muku fatan bikin Eid-fitr mai albarka da kuma Nasara na semester na biyu na 2020/2021 na ilimi.”

Zafafa Labarai