Countdown
Connect with us

Labarai

Ana zargin Jami’an Hukumar KASTELEA da cire batirin motocin masu laifi

Published

on

Jami’an KASTELEA

Jami’an Hukumar KASTELEA sun fara cire batrin motocin masu laifi, wanda Jama’a ke ganin yasaba dokar aikin su.

Wani mai anfani da kafafen sada zumunta Mai suna Farra’u Abubakar, yayi wanan korafi a shafin sa na Facebook.

inda ya walafa cewa,

” KASTELEA yanzu suna bude injini mota domin cire batirin moto, suna dauke da dukanin kayan aiki cire batirin a tare dasu, bansan wani doka ya ba ma jami’in kula da zirga zirgan ababen hawa damar cire batirin moto wanda ya saba dokar haya ba. Nasan dai suna cire numbar mota, ama banga dalili da zai sa ace suna cire batirin mota ba dan kawai suna so ka bi doka, duk da hatsarin da yin hakan wanda ka iya jawo matsala ga lafiyar mota, musaman ma ace wanda ya cire ba shi da kwarewa a fani. Ya hukunci haka yake? Shin dama akwai tsarin hakan acikin dokar aiyukan su?.

https://www.facebook.com/100001321803451/posts/5113859805334696/?app=fbl

Yayin hada wanan rahoton bamu samuji daga bakin hukumar KASTELEA ba, don jin ta bakinta akan al-amarin.

Gwamnati Elrufai ne dai ta samar da hukumar KASTELEA don lura da sha’ani kula da dokokin hanya ga masu ababen hawa a fadin jihar, tun lokacin mulkin sa na farko.

Tare da cin tara duk wanda ya saba ka’idar hanya.

Zafafa Labarai