Countdown
Connect with us

Tsaro

An kama Kansila mai wakiltar soba da Bindigar AK-47 kusa da yakin yan bindiga a Kaduna

Published

on

Jami’an Yan sanda Hoto: KOLA SULAIMON Asali: Gettyimage

An kama Kansila mai wakiltar karamar hukumar Soba a jihar Kaduna, Abdul Adamu Kinkiba da bindigar AK-47 a kusa da karamar hukumar Giwa ta jihar.

Jaridar Dailytrust, ta rawaito cewa yankin na kusa da wani sansani ‘yan bindiga da ke addabar sassan jihar.

Shugaban karamar hukumar Soba Injiniya Suleiman Yahaya Richifa ya tabbatar da kamun.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin shine kansila mai wakiltar mazabar Kinkiba a majalisar.

Sai dai ya ƙi ya yi ƙarin bayani, ya ƙara da cewa, “Ina cikin matuƙar yanayi Mara dadi game da labarin. Don Allah ku ba ni damar shawo kan kaduwata.”

Saidai jaridar dailypost tayi kokarin tuntubar jami’i Mai kula da hulda da jama’a, na rudunar Yan sanda Jihar kaduna, ASP Muhammad, inda yace Yana Kan hanyar sa ta zuwa masalaci ama zai tuntube su daga baya.

Zafafa Labarai