Countdown
Connect with us

Siyasa

Akwai Rashin Tausayi a korar malaman firamare da Gwamnati Kaduna tayi – Hon. Ashiru kudan

Published

on

Hon. Ashiru Kudan, yayi kira ga Gwamnati Jihar Kaduna da tayi hakuri ta dakatar da korar Malamai firamari datayi.

Kudan, wanda shine Dan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna a karkashin jam’iyar PDP a zaben 2023, yayi kiran ne a cikin wani gejeran sako da ya fitar.

Yace, Sam bai kamata ace anyi korar ma’aikata ba a halin da talakawa ke ciki ba, na tsanani rayuwa.

In za a tuna hukumar illimi baidaya ta Jihar Kaduna ta sanar da korar Malamai firamari sama da dubu biyu, wanda ya hada da shugaban NUT.

Kudan yakara da cewa, in har ba za a iya talafa wa al’umar Kaduna a halin da suka tsinci kansu na tsada rayuwa, to bai kamata kuma adinga rabasu da gun ayyuka su ba.

Yakara da Kiran Gwamnati Kaduna da ta da katar da korar ma’aikata da take cigaba dayi a fadin Jihar baki daya.

Zafafa Labarai