Countdown
Connect with us

Tsaro

Akwai Bukatar Gwamnati Sai Ta Kara Kaimi Wajen Gani Ansako Wanda Akayi Garkuwa Dasu A Harin Jirgin Kasa Abuja Zuwa Kaduna – Kanar Umar

Published

on

Tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kaduna, Kanar Abubakar Dangiwa Umar (rtd), ya bayyana matsayin abin tayar da hankali, Hotunan wadanda aka yi garkuwa da su bayan harin da aka kai kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kanar Umar, wanda shi ne shugaban kungiyar Movement for Unity and Progress (MUP), a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce Hotunan sun nuna yadda mata da kananan yara ke cikin mawuyacin hali.

Ya ce, “Hotunan mutanen da aka yi garkuwa da su a harin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna daga ranar 28 ga Maris Wanda ya yadu a shafukan sada zumunta.

Hotunan, a takaice, sun da tayar da hankali, musamman yadda suka nuna gajiyayyu da firgitan mata da yara a karkashin yanayi mafi muni. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wajen ganin an sako wadannan da ba su ji ba ba su gani ba.

“Ina kuma kira ga al’ummar duniya, musamman kungiyar agaji ta Red Cross, (ICRC), da su taimaka a tattaunawar da za a buƙaci don aiwatar da wannan sakin.”

Ya kuma yi addu’ar Allah ya taba zuciyar masu garkuwa da mutanen. ” Allah ya taba zukatan masu garkuwa da mutane domin su tausaya wa wadannan wadanda ba su ji ba ba su gani ba kuma wadanda abin ya shafa. Amin” Umar yace.

Zafafa Labarai