Countdown
Connect with us

Labarai

Abubakar Musa Dan Shekara Sha Tara Ya Kirkiro Jirgi Sama Mara Matuki Don Habaka Harkan Noma A Kaduna

Published

on

Musa ceo mushcreative

Musa, ayayin tattaunawa da wakilin kadunareporters ya bayana cewa, A gaskiya tun daga kuruciya shi yake matukar son kayaye kin fasaha. Kuma ya fara kirkiran kayaye kin fasahar ne tun lokacin dayake kimani dan shekara 12 zuwa 15 a duniya, duk da alokacin yana fuskanta matsalar karancin kayan aiki.

Wanda hakan ya bashi damar fara gudanar da bincike tayarda zai iya kirkiran wasu kayakin fasaha da dama, yana tsaka da bincike sai ya fara samu sha’awar fasahar kirkiran jirgi marar matuki (drone), daganan ne ya fara Tara kudi yana siyo kayayekin aiki har Allah yasa ya samu nasarar kirkiran jirgi marar matuki don habaka harkan noma.

Jirgi marar matuki daga Mushcreative

Jirgin dai ya tsara shine don saukake wa manoma aban garen feshin maganin kwari, ko kuma ban ruwa ga ma su noman rani, tare da faisa takin ruwa na zamani.

Musa, mamalakin kamfani Mushcreative, dai dan asalin Jihar Nasarawa ne a karamar hukumar Toto, ama mazauni Jihar kaduna, inda ya kamala karatun sakandirin sa a makarantar Evat dake badiko a Jihar kaduna, sai dai har yanzu Bai fara karatun Jami’a ba.

Musa ya ce, kawo yanzu ya kirkiri jirgi marar matuki zasu kai kimani guda uku, saidai yace ba iya kirkira kawai yake Yi ba ya na horar da matasa yadda ake hada jirgi marar matuka, tare da gyara jiragen in sun samu matsala da kuma basu takar Dan shaidar horo.

Damgane da kalubale kuwa, Musa yace kamar yadda kowace sana’a take da kalubale haka zaliki harka kirkiran jirgi marar matuka ke dauke dashi, sai dai shi kalu balan da yafi fuskanta shine siyo kayayekin hada jirgin wanda ba asamun su a Nijeriya.

Musa ya Kara dacewa, ada babu Mai talafa Masa, ama yanzu cibiyar bukasa har kan kasuwanci na gwamnati Jihar kaduna (KADIPA), ta gayace shi kuma tayi masa alkawarin bashi dukan talafin dayake bukata don habaka fasahar sa.

Zafafa Labarai