Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Tsohon Kwamishina Elrufai, Dattijo ya lashe zaben fidda-gwani kujerar Sanata Kaduna ta tsakiya

Published

on

Tsohon Kwamishina Elrufai, Kuma tsohon shugaban ma’aikata Gwmana Jihar Kaduna, Hon. Muhammad Sani Abdullahi, wanda akafi sanni da Datijo ya lashe zaben fidda-gwani kujerar Sanata Kaduna ta tsakiya a jam’iyar APC.

Datijjo yayin ganawa da Yan jarida Hoto: Samuel Ubile

Datijjo, ya lashe zaben ne bayen janye war abokan takara shi Usman Sani da Hajiya Rabi Salisu, kafin fara kada kuri’a a baban dakin taro Umar Musa Yar’adua dake dandali Murtala a kaduna.

Muhammad Bayero, jami’i Mai bayana sakamokon zaben, yace ana da adadin delegates guda 405 daga kanana hukumomi 7 da suka hada Kaduna ta tsakiya.

Yace delegates 396 Suka samu damar zuwa Kuma aka tantance su, bayan kamala kada Kuri’u, Datijjo ya samu Kuri’u 388 yayin da Kuri’u 8 suka lalace.

Datijjo wanda shine yasamu Kuri’u mafi rinjaye shi yayi nasara lashe zaben, cewar Bayero.

Datijjo a farko yaso yin takara kujera Gwamna Jihar Kaduna ne kafin Elrufai yabashi shawara janye wa Sanata Uba Sani, shi kuma ya nema takara kujera Sanata Kaduna ta tsakiya.

Zafafa Labarai