Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Mata 70 sun sauye sheka zuwa jam’iyar NNPP a Kaduna

Published

on

matan da suka sauya sheka zuwa NNPP a Kaduna Hoto: Kwankwasiya Reporters TV Asali: Facebook

Aqala mata daga Jami’ar PDP da APC kimani 70 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP.

Bayanin hakan na kunshe ne a wani rahoto da jaridar Kwankwasiya Reporters ta walafa a shafin ta na Facebook a safiyar litini.

Kimani mata 70 ne suka sauya sheka daga APC da PDP zuwa jam’iyar NNPP, karkashin jagoranci Hon. Ibrahim Balarabe Musa garkuwa Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kaduna, Mai wakiltar Zaria city.

Sauya sheka ba sabon Abu bane a gun yan siyasa a Nijeriya. Sanan karuwa Mata 70 zuwa jam’iyyar NNPP ba karamin nasara bace.

Jam’iyar NNPP ita ce jam’iyar da tsohon Gwamna Kano, Eng. Rabiu Musa Kwankwaso, yake takara kujerar shugaban kasa.

Zafafa Labarai