Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Ku dawo min da kudi na, Adam Namadi Sambo ga delegates bayan fadi zaben fida gwani

Published

on

Yaron tsohon mataimakin shugaban kasa Nijeriya, Namadi Sambo, ya bukaci delegates da su dawo masa da kudin sa bayan faduwa zaben fidda gwani da yayi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Adam Namadi Sambo, ya umarci delegates da su dawo masa da naira miliyan biyu (2M), daya ba wa kowanen su kafin gudanar da zaben fidda gwani.

Namadi, wanda ya fadi a zaben fidda gwani takara kujerar Dan majalisa wakilai, Mai wakilta karamar hukumar Kaduna ta Arewa, a jam’iyar PDP, ya bukaci delegates da su dawo masa da kudin sa daya basu.

Yayi alkawari kara musu naira miliyan daya da rabi (1.5M), in har ya lashe zaben, akan kudin daya basu, duk da haka yasa mu kuri’u mafi karanci acikin su uku da suka gwabza zaben.

A karshe dai Hon. Samaila Sulaiman, ne yayi nasara lashe zaben inda ya dauke Shehu ABG dakuma Adam Namadi Sambo, da kuri’u 22.

Zafafa Labarai