Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Khadija Muhammad Sani Ta Siya Fom Din Takara Majalisa Jiha, Don Wakilta Al’umar Zaria Kewaye

Published

on

Majida Muhammad Sani Hoto: Majida Asali: Facebook

A yayin da yan siyasa ke cigaba da siyan fom tin takara a zaben shekarar 2023, a jam’iyu daban daban tsaknin mata, maza datijai da matasa.

Khadija Muhammad Sani, wace akafi sanni da Majida, ta siya fom din takarar zama yar majalisa jiha, Mai wakiltar al’umar Zaria Kewaye, a Kar kashin inuwar jam’iyyar APC.

Majida ta siya fom din ne a ranar litini 9 ga watan mayu, 2023 a ofishin jam’iyar APC da ke kaduna.

Takasan ce mace Mai kishi tare da wayar da kan Mata da matasa don gani sun dagora da kan su tare da samar da abubuwan cigaba a cikin al’umah.

Yayin zan tawa da manema labarai Jim kadan bayan siyan fom, Majida, ta bayana cewa kiraye kirayen kungiyoyi Mata da matasa daga ban garori daban daban ne da bukatar ta shiga cikin farfajiyar siyasa don bada nata gudumawar, yasa ta shiga fagen fafatawa neman takara dan samar da wakilci nagari don inganta rayuwakan al’umar Zaria Kewaye.

Batun kalubalen mata a siyasa musaman a yankin arewa, Majida tace tsaya war ta baya nuni da yunkuri samar da daidai to tsakanin mata da maza, saidai akwai bukatar a dunga ba ma mata da akaga sun chanchan ta ma su jajircewa da kishi, dama domin nuna ta su bajintar a fagen siyasa.

Tuni dai Yan uwa da abokan arziki suka cigaba da farin ciki tare da murnar da mata adu’oi fatan alheri da nasara tare da nuna goyon bayan su dari bisa dari a gareta.

Zafafa Labarai