Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Kakakin Majalisa Jihar Kaduna Ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyar APC

Published

on

Rt.Hon. Yusuf Zailani, Kakakin Majalisa Jihar Kaduna Hoto: Zailani Asali: Twitter

Kakakin zauren majalisan Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Zailani, yayi nasara lashe zaben fidda gwani da aka fafata a tsakanin masu Neman takarar kujerar dan Majalisa Jihar Kaduna, mai wakilta al’umar Igabi ta yamma, Kar kashin inuwar jam’iyyar APC a kaduna.

A jiya Alhamis ne dai aka gwabza zaben fidda gwani Yan takara kujerar yan majalisa jihohi a karkashin inuwar jam’iyyar APC a kasa baki daya, Cikin wanda suka gwabza a Igabi ta yam’ma sun hada da Abdullahi Musa, Salamatu Musa Yuguda.

Sakamokon zaben sun nuna cewa kakakin Majalisa, ya samu kuri’u 28 sai Abdullahi Musa dake binsa abaya da Kuri’u 1 , yayin da Salamatu Musa Yuguda bata samu Kuri’u ko guda ba.

Zailani, wanda ya shafe shekaru da dama a zauren majalisa Jihar Kaduna, kafin zaman sa Kakakin Majalisa a shekara 2020.

Zafafa Labarai