Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Hon. Samaila Suleiman ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyar PDP

Published

on

Hon. Samaila Sulaiman Hoto: Mal. Samaila Sulaiman Asali: Facebook

Rohotonin sun bayana cewa Hon. Samaila Sulaiman, shine ya lashe zaben fidda gwani jam’iyar PDP, na dan majalisa mai wakilta al’umar Kaduna ta arewa.

Sulaiman, ya samu lashe zaben ne da kuri’u 20, yayin da abokan takaransa Shehu Usman ABG, ya samu kuri’u 14, sai kuma Baffa Namadi Sambo, yasamu kuri’u 2. Kamar yadda ya bayana a sakamokon zaben.

A ranar lahadi ne dai aka yi zaben inda Hon. Sulaiman, ya lashe zaben wanda hakan ya ba shi dama yin takara sau uku kenan a jere tundaga zaben 2015, 2019 da Kuma 2023.

Sulaiman, dai ya fara da zama shugaban karamar hukuma ne, daga bisani yayi nasara lashe zaben 2015 inda yazama Dan majalisan a jam’iyar APC da Kuma 2019.

Kwana ki bayane dai Sulaiman, ya bayana ficewar sa daga jam’iyar APC zuwa PDP, in da ya bayana cewa, “ya bar jam’iyar APC ne sabida rikicin da ke faruwa a jam’iyar.”

Zafafa Labarai