Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Hon. Ashiru Kudan ya dauki Dr John Markus Ayuba a matsayin mataimaki

Published

on

Dan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna a karkashin jam’iyar PDP Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan, ya dauki Dr John Markus Ayuba, ya Zama masa mataimaki a zaben 2023.

Shuibu Gimi, Mai bada shawara kan harkar sadarwa na Dan takara ya bayana hakan a wata sanarwa da yafitar.

Yace zabin Dr Ayuba ya biyo bayan tattaunawa da ma su ruwa da tsaki Jam’iyar PDP, musaman wanda suke zaune a kudancin Kaduna.

Ayuba shine shugaban masu ruwa da tsaki Jam’iyar PDP na Karamar Hukumar Zangin Kataf, kuma malamin jami’a, tsohon ma’aikaci banki kuma tsohon Kwamishina kudi, wanda yabada matukar gudun mawa ga jam’iyar PDP.

Kudan ya taya mataimaki nasa murana tare da kira ga dukan Yan jam’iyar PDP da su karbi zabi, tare da aiki gun gani jam’iyar tayi nasara.

Zafafa Labarai