Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Elrufai ya bayana goyon bayan sa ga Tinubu Kan neman kujerar shugaban kasa

Published

on

ziyarar Tinubu a kaduna Hoto: Ahmed Tijjani Ramalan Asali: Facebook

Gwamna Jihar kaduna, Malam Nasiru Elrufai, ya bayana goyon bayan sa da Neman takarar shugaban kasa da jagoran APC Ahmed Bola Tinubu, ya keyi.

Elrufai, ya bayana na hakan ne a dadalon Murtala Square dake cikin birnin Jihar kaduna, a lokacin da Tinubu, ya kawo ziyara jihar a ranar Alhamis.

Tinubu, ya sa mu rakiyar tsohon gwamna Borno, Kashim Shattima, tsohon shugaban EFCC,Nuhu Ribadu, tare da wasu jiga jigan matune don neman amincewar delegates.

Anasa jawabin, Shattima, ya bayana wa delegates din Jihar kaduna cewa” Gwamna Elrufai Yana tare dasu dari bisa dari.”

A lokacin da yake jawabi, Elrufai, ya fadawa Shattima, cewa dole yana bukatar jin ra’ayin delegates kafin yenke hukunci marawa Tinubu, baya.

” Don tabatar da maganar Shettima, Elrufai, ya tambaye daligates din dake gurin cewa ko suna tare da Tinubu? Inda Suka amsa dacewa Eh suna tare dashi Kuma a shirye suke sumara masa baya.

Zafafa Labarai