Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: Delegates din da suka karbi kudi yayin zaben fidda-gwani APC sun fara danasani – Amaechi

Published

on

Tsohon Minista Sufuri, Rotimi Amaechi, yace duk delegates din da suka karbi kudi lokacin zaben fidda-gwani na kujerar shugaban kasa a jam’iyar APC sun fara danasani.

Amaechi yace dukan delegates da kudi ya rufe musu ido a lokacin zaben sun fara danasani.

Tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa ya bayana hakan ne a gurin bikin cika Shekara 60 na Apostle Eugene Ogu, General Overseer of Abundant Life Evangel Mission, wanda ya gudana a garin Fatacut na jihar Rivers.

Ya kara dacewa bada kudi domin samun kuri’u ba zaitaba sauya matsalar Nijeriya ba.

Amaechi yayi kira ga limamai da suyi adu’a ga ‘yan Nijeriya domin gani sun zabi shuganin nagari da zasu kawo karshen matsaloli da kasar ke fama dashi.

Amaechi ya bayana cewa, ” Su waye, wanda da sukayi zaben firamari na APC ? Ai ‘yan Nijeriya ne. Kudin da suka karba ya kawar musu kawai da matsalolin su na lokacin ne, ama yanzu suna fadin sunyi kuskure. Labarai daban daban kawai akeji.

” In zaku mana adu’oi to kuyi wa shuwagabanin mu sanan kuyi wa ‘yan kasa adu’a domin su zabi shugaban kasa nagari wanda zai mulke kasar.

” Bada kudi bashi ne zai kawar da matsalar Nijeriya ba, dole sai kowa ya tashi mun hada kai sanan zamu magance matsalar Nijeriya.”

Zafafa Labarai