Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: delegate ya kashe wa marayu Miliyan 13 daga kudin da yasamu a zaben fidda-gwani PDP na shugaban kasa

Published

on

Wani delegate ya Sha yabo bayan kashe wa al’umar sa kudi da yayi, cikin kudaden daya samu a zaben fidda-gwani kujerar shugaban kasa na Jam’iyar PDP da aka kamala….

Tanko Rossi Sabo, dan karamar hukumar Sanga a Jihar Kaduna, yace ya kashe wa al’umar sa kudaden ne sabida yaga suna da bukata mataku.

Ya bayana haka ne yayin zantawa da jaridar The Gazette ta wayan tarho a ranar laraba.

“Na biya kimani naira miliyan 13 ga marayu 150 akan sha’ani karatun su, tare da biyan kudin asibiti ga tsoffi tare da wasu abubuwa da dama.

Ina matukar farinciki na taimaki al’uma ta daga cikin kudin da nasamu a gurin zaben fidda-gwani.”

Mr Sabo, na daya daga cikin delegates 800 a fadin Nijeriya, da suka gudanar da zabe fidda-gwani kujerar shugaban kasa na Jam’iyar PDP a ranar 29 ga watan Mayu, 2022 wanda Atiku Abubakar ne ya lashe zaben.

Sabo ya Kara da cewa, ” Tunda na isa Abuja wasu yan takara ke ta kirana, wasu suka bani dubu dari hudu zuwa dari biyar domin naje na kwana a makwanci mai kyau. Ni kimu na kwana a mota ta mai makon kwana a makwanci Mai kyau.

Zafafa Labarai