Countdown
Connect with us

Siyasa

2023: daligates 300 ne ke ikirarin su suka bani kuri’a biyu da nasamu – Shehu Sani

Published

on

Dan takara kujerar Gwamna Jihar Kaduna a jam’iyar PDP, Shehu Sani a ranar Alhamis, ya bayana cewa duk da Kuri’u biyu na sa mu yayin zaben fidda gwani ama kawo yanzu delegates 300 ne suka kira ni suna ikirarin sune suka zabe ni…

Sanata Shehu Sani

Biyo bayan kamala zaben fidda gwani na yan takara kujera Gwamna Jihar Kaduna a karkashin jam’iyar PDP, wanda Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan, ya lashe da Kuri’u 414, yayin da Sanata Sani ya samu Kuri’u biyu kachal.

Sani ya bayana haka a wani rubuta da ya walafa a shafin sa na Twitter cewa;

” Delegates biyu ne suka zabe ni ba tare da na Basu ko kobo ba; kawo yanzu delegates 300 ne suka kirani suna ikirarin cewa su ne suka zabe ni suna so suzo su gani. Wanan wani kalar wahala ce….”

Tun kafin ranar zaben Sanata Sani, ya sha alwashin ba zai ba da ko ficika ga delegates ba domin su zabe shi.

Bayan Kamala zaben ne, ya yi matukar farinciki da Kuri’u biyu da yasa mu, inda yace ya chanchanchi yayi wa delegates din da suka zabe shi godiya, sun zabe shine domin ganin ya chanchanta ba wai don ya basu kudi ba sai dai bai San su ba.

Zafafa Labarai